Anyi kira da Buhari da Tinubu su takawa Oshiomhole birki

Anyi kira da Buhari da Tinubu su takawa Oshiomhole birki

- Ana zargin Ciyaman din APC na kasa Adams Oshiomhole da kakabawa mutanen yankin Delta ta Kudu dan takarar Sanata ba tare da zaben fidda gwani ba

- Hakan yasa wata mai rajin kare hakkin bil adama, Lori-Ogebebor ta yi kira da Buhari da Tinubu su tsawata wa Oshiomhole

- Ta yi ikirarin cewar Oshiomhole ne ya ke kokarin kakabawa al'ummar yankin tsohon gwamna Emmanuel Uduaghan a matsayin dan takara

Wata mai rajin kare hakkin bil adama, Cif Rita Lori-Ogebebor ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da Jagoran Jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu su tursasa wa Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ya soke zaben fidda gwani da aka yi a yankin Delta ta Kudu.

Anyi kira da Buhari da Tinubu su takawa Oshiomhole birki

Anyi kira da Buhari da Tinubu su takawa Oshiomhole birki
Source: Twitter

Ta yi gargadin cewar rashin soke zaben zai iya kawo tashin hankali a yayin gudanar da babban zaben kasa na 2019 a yankin.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

A yayin hirar da tayi da manema labarai jiya a Legas, Lori-Ogbebor ta bukaci a sake gudanar da zaben fidda gwanin domin a cewarta an Oshiomhole ya kakabawa mutanen jihar tsohon Gwamna Emmanuel Uduaghan a matsayin dan takarar Sanata.

Lori-Ogbebor ta yi ikirarin cewar ba'a gudanar da zaben fidda gwani ba a jihar domin dukkan 'yan takarar kujerar Sanata na yankin wanda suka hada da Air Vice Marshal Okorodudu, Temisan Omatsye da sauransu sun kira ta a waya sun shaida mata babu wanda suka gani a filin kada kuri'ar.

Ta kara cewa daga baya kwatsam kawai sai suka ji sanarwar cewa tsohon Gwamna Uduaghan ne ya lashe zaben kuma ta yi kokarin tuntubar Oshiomhole a wayar tarho domin jin bahasi amma hakan bai yiwu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel