Akwai yiwuwar Zidane ya maye gurbin Mourinho a Man United amma da sharadi

Akwai yiwuwar Zidane ya maye gurbin Mourinho a Man United amma da sharadi

Bisa dukkan alamu dai, akwai yiwuwar Zinedine Zidane ya maye gurbin Jose Mourinho a Kungiyar Man United kamar yadda labarai su ke zuwa mana daga Jaridun kasar nan da kuma ma na cikin Turai.

Akwai yiwuwar Zidane ya maye gurbin Mourinho a Man United amma da sharadi

Zidane yace dole ya rika zaben ‘Yan kwallon da yake so a United
Source: Twitter

Yanzu dai Kocin Manchester United Jose Mourinho yana cikin tsaka-mai-wuya inda yake kasa a teburin Firimiya kuma har an yi waje da shi daga wani karamin kofi a Ingila. Haka kuma Man Utd ta gaza cin wasan ta na Turai kwanaki.

Hakan ya sa babban Kulob din na Manchester United ta fara zawarcin Zinedine Zidane wanda yayi abin a yaba a Kungiyar Real Madrid. Sai dai kuma yanzu Man United ta na fama da kalubalen amincewa da sharudan da Zidane ya kakaba mata.

KU KARANTA: Ana neman ciwo wa Najeriya sabon bashin tiriliyan daya

Kocin ‘Dan asalin Kasar Faransa na neman ba Kungiyar ta Ingila ciwon kai kwarai da gaske kafin yayi amanna da aiki da su. Zidane dai ya gindayawa Kulob din wasu tarin sharuda ne wanda dole sai an cika masa kafin ya dawo Ingila da wasa.

Jaridar The Independent tace yanzu ya ragewa Ed Woodward wanda shi ne babban Jami’in Kulob din ya amince da bukatun Zidane. Daga cikin bukatun tsohon Kocin na Real Madrid shi ne a kyale sa yayi ruwa da tsaki wajen sayayyen 'Yan wasa.

Yanzu dai ya ragewa Woodward wanda kusan shi yake sayowa United ‘Yan wasa yayi na’am da wannan bukata. A Madrid dai ba a ba Zidane damar sayo manyan ‘Yan wasan da ya ga dama ba ko kuma kyale sa wajen saida na sa manyan 'Yan wasan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel