Ba za mu tsige Dogara ba – Babban jigon APC

Ba za mu tsige Dogara ba – Babban jigon APC

Bulaliyar majalisar wakilai, Alhassan Doguwa, ya karyata rade-radin dake yawo kan yiwuwar tsige kakakin majalisa, Yakubu Dogara.

Ana sanya ran za tsige mista Dogara wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa babban jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) kamar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Jim kadan bayan sauya shekarsa, APC ta ce lallai sai Mista Dogara ya yi murabus ko kuma ya shirya tsige shi.

Ba za mu tsige Dogara ba – Babban jigon APC

Ba za mu tsige Dogara ba – Babban jigon APC
Source: Twitter

A nashi ganin Mista Doguwa yace kakakin majalisar na da ikon komawa duk jam’iyyart siyasar da yake muradi.

Bulaliyar majalisar ya ci gaba da cewa sauya sheka bai saba ma kowani sashi na dokar majalisa ko kundin tsarin mulkin Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Bukola Saraki ya nada kwamiti domin duba dalilin da ya sa Buhari yayi watsi da kudirin su

Ya bayyana ofishin kakakin majalisa da na mataimakinsa a matsayin wanda mamba na kowace jam’iyya zai iya jagoranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel