Bukola Saraki ya nada kwamiti domin duba dalilin da ya sa Buhari yayi watsi da kudirin su

Bukola Saraki ya nada kwamiti domin duba dalilin da ya sa Buhari yayi watsi da kudirin su

Mun samu labari dazu daga Jaridar Daily Trust cewa Bukola Saraki ya nada kwamiti a Majalisa domin duba ainihin dalilin da ya sa Shugaban kasa yayi watsi da kudirorin da Majalisar Tarayya ta aika masa.

Saraki ya nada kwamiti domin duba dalilin da ya sa Buhari yayi watsi da kudirin su

An sa kwamiti a Majalisa bayan Buhari yayi watsi da kudiri 16
Source: Depositphotos

A makon nan ne Majalisa ta samu labari cewa an yi fatali da wasu kudirori har 16 da ta aikawa fadar Shugaban kasa. A dalilin haka ne Sanatoci su ka nada kwamiti karkashin Sanata Baba Kaka Garbai domin duba lamarin.

Sanata Baba Garbai wanda shi ne Shugaban kwamitin dokokin Majalisa da wasu Sanatoci ne za su yi wannan aiki inda za su fede hujjojin da Shugaban kasa ya bada na yin watsi da tarin kudirin da aka aika masa ya sa hannu.

Shugaban kasa dai bai amince da kudirorin da Majalisar Dattawan ta kawo masa ba ne inda ya bada dalilan sa na kin sa hannu. Daga cikin dalilan da Shugaba Buhari ya bada akwai batun rashin hurumi da iko a tsarin mulkin kasa.

KU KARANTA: Sanata Shehu Sani ya amsa kalubalen Gwaman El-Rufai

Sanata Ahmad Lawan wanda shi ne Shugaban masu rinjaye a Majalisar ya nemi Sanatocin kasar su duba wasikun da takardun da Shugaban kasa ya aiko domin fahimtar kure-kuren da su ke ciki da kuma garambawul din da za ayi.

Yanzu dai wannan kwamiti da za a kafa za ta sake duba kudirorin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattabawa hannu. Daga cikin wannan kudirori akwai wanda Majalisar ta aikawa Shugaban kasa game da tsarin zabe

Dazu kun ji labari cewa Bukola Saraki zai karasa wa’adin sa a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa bayan Sanatocin APC sun yi watsi da umarnin da Jam’iyya ta ba su na shirin tunbuke Sarakin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel