Ma’aikata su na neman Gwamnatin Tarayya ta sauke Shugaban NHIS

Ma’aikata su na neman Gwamnatin Tarayya ta sauke Shugaban NHIS

Mun ji cewa Manyan Ma’aikata a Hukumar NHIS sun nemi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sallami Shugaban Hukumar watau Usman Yusuf inda su ke zargin sa da rashin gaskiya a wani karon.

Ma’aikata su na neman Gwamnatin Tarayya ta sauke Shugaban NHIS

An nemi Gwamnati ta sake cire Shugaban NHIS Usman Yusuf
Source: Facebook

A jiya ne Manyan Ma’aikatan da ke aiki karkashin Usman Yusuf su ka nemi Gwamnatin Tarayya ta sake koran Shugaban na NHIS wanda aka taba dakatarwa daga aiki kwanakin baya a dalilin zargin sa da aikata rashin gaskiya da barna.

Ma’aikatan Hukumar sun yi kira cewa ya kamata Shugaban na su ya ajiye wannan aiki har kuma ayi binciken gaskiyar lamarin abin da ke faruwa a NHIS. Isaac Ojemhenke ne Ma’aikacin da yayi magana a madadin sauran Abokan aikin sa.

A baya dai Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewole ya kori Usman Yusuf kafin Shugaban kasa da kan sa ya maido sa bakin aiki. Jama’a da dama dai ba su ji dadin hakan ba duk da cewa Shugaban na NHIS ya wanke kan sa a bainar Jama’a.

KU KARANTA: Kungiyar NUT ta roki Gwamnati ta biya malamai albashi

Wannan karo dai Ma’aikatan Hukumar sun kira taro a gaban Sakatariyar Kungiyar inda su ka bayyana cewa Shugaban na NHIS yana da kashi a jikin sa. Ma’aikatan su na zargin sa da laifuffuka har 8 na satar dukiyar Gwamnatin Najeriya.

Daga cikin laifin da ake zargin Yusuf da aikatawa akwai karkatar da kudi har Miliyan 3.6 wajen sayen fetur a lokacin da aka dakatar da shi daga aiki. Sannan kuma ana zargin Shugaban da ba kamfanin ‘Yan uwan sa kwangilar Miliyoyi.

Ma’aikatan kuma su na zargin Usman Yusuf da biyan kan sa alawus din bogi da kuma karkatar da wasu kudi har Naira Biliyan 25 na masu amfana da tsarin NHIS a kasar jim kadan bayan ya shiga ofis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel