Kananan yara 59, 000 ne ke rasa rayukansu a sanadiyyar amai da zawo a Najeriya

Kananan yara 59, 000 ne ke rasa rayukansu a sanadiyyar amai da zawo a Najeriya

Alkalumma daga hukumomin gwamnatin tarayya sun tabbatar da kimanin kananan yara dubu hamsin da tara ne suke mutuwa a sanadiyyar barkewar cutar amai da zawo a kowanne shekara a Najeriya, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Ministan ruwa, Suleiman Adamu ne ya sanar da haka a ranar Talata 9 ga watan Oktoba a yayin ganwa da manema labaru don bikin ranar wanke hannu ta duniya, inda yace cutar amai da zawo na barkewa ne sakamakon kazantar muhalli da na ruwan sha.

KU KARANTA: Wata yar Najeriya ta halaka kanta bayan gwamnatin kasar Ghana ta garkame mata shago

Ministan ya kawo wasu alkalumma daga cibiyar bincike ta WashWach da suka nuna cewa kimanin kashi 33 na kananan yara yan kasa da shekaru biyar a Najeriya sun daina girma sakamakon ire iren cututtukan dake samuwa daga rashin tsafta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan ya kara da cewa alkalumma sun nuna kasha 87 na yan Najeriya basu da kayan wanke hannuwa, duk da cewa suna da sabulu da ruwa a yankunansu.

“Rashin ababen wanke hannu da suka hada wajen wanke hannu a makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya da kuma wuraren aiki yana rura matsalar nuna bambancin tsakanin mata da yan mata, musamman game da tsaftace a yayin jinin haila.” Inji shi.

Wannan ne yasa ma’aikatar ruwa ta shirya hidindimu don tunawa da wannan rana ta wanke hannu da suka hada da ziyarar wayar da kai game da wanke hannuwa a sansanon yan gudun hijira guda takwas dake Abuja a ranar Asabar, taron koyar da wanke hannu a Abuja a ranar Litinin, da kum taron kiwon lafiya da shuwagabannin mayanka, kasuwanni da kungiyoyin addinai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel