‘Yan Majalisa sun hakura da batun tsige Shugabannin Majalisar Tarayya

‘Yan Majalisa sun hakura da batun tsige Shugabannin Majalisar Tarayya

Dama dai Hausawa su na cewa duk fadan da ya fi karfin ka maida sa wasa, don haka ne ma mu ke jin kishin-kishin din cewa Sanatocin APC sun yi fatali da umarnin Jam’iyya na tsige Bukola Saraki.

‘Yan Majalisa sun hakura da batun tsige Shugabannin Majalisar Tarayya

Akwai yiwuar Bukola Saraki zai kammala wa’adin sa har 2019
Source: Depositphotos

Duk da cewa Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma rinjaye a Majalisar Tarayya ta nemi ‘Yan Majalisan su yi yunkurin tsige Bukola Saraki daga kujerar sa, Sanatocin dai sun ja baya da yin wannan aiki inji Jaridar The Cable.

Jam’iyyar APC ta hurowa Bukola Saraki wuta cewa ya bar kujerar sa na Shugaban Majalisar Dattawa tun da ya sauya-sheka zuwa PDP kwanaki. Sai dai wata Majiya daga Majalisar kasar ta bayyana cewa zai yi wahala a taba Saraki a yanzu.

Wani Sanatan APC da sunan sa ba bako bane Ovie Omo-Agege, ya fadawa ‘Yan jarida cewa za a cire Saraki daga matsayin na sa kuma a fi da zaman lafiya. Sai dai zaman da Majalisar tayi a jiya bayan dogon lokaci ya nuna akasin haka.

KU KARANTA: Oshiomhole ya kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - inji Saraki

Kusan ma dai Sanatocin da ake ji da su a APC sun nemi a zauna lafiya ne tare da Bukola Saraki wanda yake rike da Majalisar Tarayyar. Akwai yiwuwar ma anyi yarjejeniya cewa babu wanda zai yi gigin tsige Bukola Saraki daga kujeran sa.

Sanatocin na Jam’iyyar APC Sun amince su yi aiki da Saraki ba tare da kawo masa wata matsala ba har zuwa lokacin da wa’adin sa zai cika. Hakan ne dai zai bada dama Majalisar da shugabannin ta ke hannun PDP ta zauna lafiya a kasar.

Kun san cewa Sanatoci sun yi zaman musamman na kokarin tsige Saraki a Majalisar Dattawa a farkon makon nan. Sai dai Atiku da wasu a PDP sun dage wajen hana wannan shiri yayi nasara a Majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel