Wani sabon rikici tsakanin al'umma ya salwantar da rayukan Mutane 17 a jihar Kogi

Wani sabon rikici tsakanin al'umma ya salwantar da rayukan Mutane 17 a jihar Kogi

Mun samu rahoton cewa kimanin rayukan mutane 17 suka salwanta a wani sabon rikici da ya auku tsakanin al'ummomin garin Bassa Kwomu da Egbura Mozum dake karamar hukumar Bassa a jihar Kogi dake Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa, rikicin wanda ya fara kunno kai tun a watan Afrilun da ya gabata, ya sake sabunta da sanyin safiyar ranar Litinin din da ta gabata, inda matasan al'ummomin biyu dake karamar hukumar Bassa.

Artabun wannan rikici da ya ci gaba har yammacin ranar ta Litinin ya salwantar da rayukan mutane 17 a yankunan wanda mafi akasarin matasa ne.

Wani sabon rikici tsakanin al'umma ya salwantar da rayukan Mutane 17 a jihar Kogi

Wani sabon rikici tsakanin al'umma ya salwantar da rayukan Mutane 17 a jihar Kogi
Source: Facebook

Al'ummomin dake makotaka da garuruwan Ketechi da kuma Ojoh sun nemi mafaka a babban ofishin hukumar 'yan sanda dake garin Oguma.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ta ruwaito, wani Matashin Yarima na garin Mozum, Shua'aibu Abubakar, ya halaka yayin wannan rikici yayin da yake kan hanytarsa ta dawowa daga Su a garin Oguma.

KARANTA KUMA: Najeriya na da bukatar Jagora mai masaniyar tattalin arziki - Obasanjo

Wani dan majalisar dokoki na jihar, Honarabul Sunday Shigaba, ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari, inda yayi kira ga hukumomin tsaro akan su gaggauta kai dauki domin kwantar da tarzoma.

Sai dai a yayin tuntubar kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Ali Janga, ya musanta aukuwar wannan rikici tare da shawartar al'ummar kan watsi da yada jita-jita da kanzon kurege.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel