An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

- Hukumomin tsaro a kasar India, sun bukaci jami'an tsaro na kasar, da su rage yawan sakin fuska a yayin da suke kan bakin aiki

- Sun bayyana cewa yawan fara'ar jami'an tsaro ne ya jawo yan ta'adda suka samu damar kai harin 9/11 a kasar Amurka

- Sun bukaci jami'an tsaron kasar, da su maida hankali kan bada kulawa ga tsaro ba tare da fara'a ko nuna sanayya ba

Hukumomin tsaro a kasar India, sun bukaci jami'an tsaro na kasar, musamman wadanda ke kula da filayen sauka da tashin jiragen sama da ke a fadin kasar, da su rage yawan sakin fuska a yayin da suke kan bakin aiki.

Hukumomin tsaron sun bayyana cewa yawan sakin fuska da fara'a da jami'an tsaron ke yi, na iya zama wata kafa ta baiwa 'yan ta'adda damar kaddamar da ta'addancinsu, wanda hakan babbar barazana ce ga lamuran tsaron kasar.

Wannan bukatar ta fito ne daga hukumar da ke kula da tsaro a tashoshin sauka da tashin jiragen sama ta kasar India, wacce ke son jami'anta su mayar da hankulansu kacokan ga tsaron kasar ba tare da nuna sanayya ko sakin fuska ba.

KARANTA WANNAN: Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki

An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya

An bukaci jami'an tsaro su rage yawan fara'a ko nuna sanayya
Source: UGC

Hukumar ta dauki wannan matakin shawarar ne a tunaininta, babu wani alfanu da sakin fuskar jami'an tsaro zai haifar illa ma ya zama hatsari ga tsaron tashoshin jiragen saman kasar.

Shugaban hukumar ya ce ta yawan sakin fuskar jami'an tsaro ne har yan ta'adda suka samu damar kai harin 9/11 a kasar Amurka wanda ya yi sanadin mutuwar mutane ba adadi da janyo asarar dukiya mai dumbin yawa.

Da wannan ne yasa hukumar tsaron ta bukaci jami'an tsaron kasar India, da su sauya yanayin mu'amalarsu da jama'a musamman ta hanyar rage yawan fara'a da nuna sanayya.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel