Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki

Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki

- Bukola Saraki ya ce Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC

- Ya ce APC na firgita da shiga rudani da zaran sunji sunan Saraki

- Haka zalika Saraki ya yi ikirarinncewa zuwa yanzu APC na cikin mawuyacin hali sakamakon kaskancin da Oshiomhole da Nabena suka jefata a ciki

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, a ranar talata ya ce shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole tare da kakakin jam'iyyar, Yekini Nabena, sun kunna wutar rikicin yakin basasa a cikin jam'iyyar ta hanyar munanan kudurorinsu.

Saraki ya kuma ce Oshiomhole da Nabena sun durkusar da jam'iyyar zuwa kaskanci wanda ya sa jam'iyyar a yanzu ke cikin rudani da tarwatsewar hadin kan mambobinta.

Jawabin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hannun mashawarcin shugaban majalisar dattijai ta fuskar watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, mai taken "Martani ga dambarwar APC".

Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki

Oshiomhole da Nabena sun kunna wutar yakin basasa a cikin jam'iyyar APC - Saraki
Source: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Kungiyar NUT ta roki gwamnatin Rivers da ta biya malaman jihar Albashi da hakkokinsu

Sanarwar ta ce: "Muna samu wata sanarwa maras da'a a ciki, da kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena ya bayar. Mu munsan cewa da shi da shugaban jam'iyyar na kasa na cikin tashin hankali da firgici da zaran sunjii sunan Saraki. Haka zalika Nabena da APC har kullum na bakin ciki da duk wani ci gaba da PDP take samu.

"To sai dai, muna da yakinin cewa yakin basasar da Adams Oshiomhole da Yakeni Nabena suka kunna a cikin jam'iyyar APC da kuma wulakancin da suka jawa jam'iyyar, a wannan yanayin, dole su kasance cikin rudani da rashin hadin kai, duk da haka, sun yi kadan su shigarwa Saraki ko PDP hanci da kudundune."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel