Najeriya na da bukatar Jagora mai masaniyar tattalin arziki - Obasanjo

Najeriya na da bukatar Jagora mai masaniyar tattalin arziki - Obasanjo

A ranar Talata da ta gabata ne tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya jadadda matsayarsa da cewa a halin yanzu Najeriya na da bukatar jagora mai kyakkyawar fahimta ta fuskar tattalin arziki da zai kai ta zuwa ga tudun tsira.

Obasanjo yake cewa tsohon shugaban kasar Jamus, Marigayi Helmut Schmidt, wanda ya kasance daya daga cikin aminansa na kasashen ketare, shi ya zayyana masa hakan yayin wata ganawa kan al'ammuran da suka shafi kasashen dake nahiyyar Afrika.

Yake cewa ba bu wata hanya da Najeriya zata fidda kan ta zuwa tudun tsira ta fuskar kyautatawa al'ummarta matukar ba shugaban kasa mai jagorancin ta ke da nakasun fahimta ta tattalin arziki.

Najeriya na da bukatar Jagora mai masaniyar tattalin arziki - Obasanjo

Najeriya na da bukatar Jagora mai masaniyar tattalin arziki - Obasanjo
Source: Instagram

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wata lacca da aka gudanar a babban cocin kasa dake unguwar Yaba a tsohon babban birnin kasar nan na jihar Legas.

KARANTA KUMA: Rikicin Makiyaya: Kada ka siyasantar da rayukan mu - Yarbawa sun yiwa Tinubu gargaɗi

Ya kara da cewa, muddin Najeriya ta na da muradin ficewa daga kangin da ta take ciki a halin yanzu dole kuwa sai ta sanya ababen duba da kuma lura wajen inganta tattalin arziki, siyasa gami da gasgatuwar imani a zukatan al'ummarta.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani hazikin Matashin ya nufi babban birnin kasar nan na tarayya akan sawayensa daga garin Zaria domin bayyana murnarsa ta nasarar tsohon mataimakin shugaban, Atiku Abubakar da ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel