Babu wani yanki na Najeriya da za’a yasar a karkashin kulawa na - Buhari

Babu wani yanki na Najeriya da za’a yasar a karkashin kulawa na - Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 9 ga watan Oktoba a Abuja yayi alkawarin cewa babu wani yanki na Najeriya da za’a yasar a karkashin kulawarsa.

Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karbi bakuncin tawagar masarautar Ugep, Cross River karkashin jagorancin Obol Ofem Ubana, Obol Lopon na Ugep, jami’in soja mai ritaya.

Shugaba Buhari na martani ne ga bukatar basaraken na cewa gwamnatin tarayya ta sanya baki wajen kawo karshen rikicin kabilanci dke faruwa a garuruwa da dama kamar irin su Nko, Nyima, Oyadama, Edibe, Usumtong, Adadama da kuma Ekureku.

Babu wani yanki na Najeriya da za’a yasar a karkashin kulawa na - Buhari

Babu wani yanki na Najeriya da za’a yasar a karkashin kulawa na - Buhari
Source: Twitter

Shugaba Buhari ya fada ma tawagar cewa: “Ina baku tabbacin cewa a karkashin kulawa na, babu yankin Najeriya da za’a yasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere

Ina burin sanar da ku cewa ina da kwarewa sosai a matsayina na tsohon jami’in soja.

“Aikin da nayi na soja ya bani damar yin aiki da dukkanin ýan Najeriya na tsawon lokaci.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel