Rikicin Makiyaya: Kada ka siyasantar da rayukan mu - Yarbawa sun yiwa Tinubu gargaɗi

Rikicin Makiyaya: Kada ka siyasantar da rayukan mu - Yarbawa sun yiwa Tinubu gargaɗi

Mun samu rahoton cewa wata kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere, ta yi tir gami da wus dangane da furucin Asiwaju Bola Tinubu, jigo kuma kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC da ya nemi gwamnatin tarayya akan ta tanadi wuraren kiwo ga makiyaya.

Tinubu wanda a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani babban taro ya nemi gwamnatin tarayya aka ta tanadi wuraren kiwo ga makiyaya cikin yankunan kasar nan da ba wani amfanar su ke a halin yanzu.

Kungiyar ta bayyana cewa, Tinubu yana da duk wata dama da kuma 'yanci na cin karen sa ba bu babbaka cikin harkokin siyasar kasar nan amma kada ya kuskura ya yi wasa da rayukan su cikin wannan lamari.

Rikicin Makiyaya: Kada ka siyasantar da rayukan mu - Yarbawa sun yiwa Tinubu gargaɗi

Rikicin Makiyaya: Kada ka siyasantar da rayukan mu - Yarbawa sun yiwa Tinubu gargaɗi
Source: Depositphotos

Kungiyar ta kausasa harshe dangane da furucin Tinubu da ya bayyana cewa, hare-haren makiyaya na aukuwa ne a sanadiyar karancin wuraren kiwo da kuma karancin ruwan sha ga dabbobin makiyaya.

KARANTA KUMA: 'Yan fashi da Makami sun kar wani Sufeton 'Yan sanda a Kudancin Najeriya

Cikin martani da sanadin kakakin ta, Yinka Odumakin a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana cewa, ba bu wani abu da tsohon gwamnan na jihar Legas ya kudirta face sanya kungiyar Miyetti Allah ta makiyaya kan hanyar mayar da dukkanin kasar nan wuraren kiwo.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Tinubu yayin halatar wani taro kan tabbatar da zaman lafiya a kasar nan da kafofin watsa labarai suka nauyin shiryawa ya bayyana cewa, tanadar wuraren kiwo ga makiyaya shi zai magance barazana da kuma aukuwar rikicin tsakanin makiyaya da manoma musammam a Arewa ta Tsakiya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel