Ma'aikata 4,042 da gwamnatin Kaduna ta kora daga aiki sun maka El-Rufai kotu

Ma'aikata 4,042 da gwamnatin Kaduna ta kora daga aiki sun maka El-Rufai kotu

Kotun masana'antu da ke da zama a Kaduna, ta dake sauraron karar da wasu ma'aaikatan kananan hukumomi su 4,042 da suka shigar da gwamnatin jihar na bukatar a mayar da su bakin aiki.

Ma'aikatan da lamarin ya shafa sun maka gwamnatin jihar kotu tun bayan da aka koresu daga aiki a watan Juwambar 2017, inda suka bukaci kotun da ta baiwa gwamnatin jihar umurnin mayar dasu aiki tare da biyansu dukkanin hakkokin da irin asarar da suka tafka sakamakon wannan danyen hukunci da gwamnatin ta yanke a baya.

Ma'aikata 4,042 da gwamnatin Kaduna ta kora daga aiki sun maka El-Rufai kotu

Ma'aikata 4,042 da gwamnatin Kaduna ta kora daga aiki sun maka El-Rufai kotu
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa karar wacce aka shorya sauraronta a wannan talatar, an dage ta saboda rashin zuwan alkalin, mai shari'a Sanusi Kado.

DUBA WANNAN: Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'

Wata jami'ar kotun, Happiness Luka, ta shaidawa bangarorin guda biyu da ke shari'ar cewar alkalin ya garzaya Abuja don halartar sallar zana'idar wani abokin aikinsa, mai shari'a Waziri Abayo, wanda ya rasu a wannan rana.

Ta ce za a sanar da su sabuwar ranar da za a ci gaba da sauraron shari'ar ba da dadewa ba.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel