Osinbajo ya shiga bayan labule da Gwamna Bindow

Osinbajo ya shiga bayan labule da Gwamna Bindow

A yau Talata, Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi wata ganawar sirri da gwamna Muhammadu Bindow na jihar Adamawa a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewar taron ba zai rasa nasaba da rikicin da ya barke a jam'iyyar All Progressives Congress APC reshen jihae Adamawa cikin kwanakin nan ba.

Gwamna Bindow ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar a ranar 7 ga watan Oktoba inda ya samu kuri'u 193,656.

Osinbajo ya shiga bayan labule da Gwamna Bindow

Osinbajo ya shiga bayan labule da Gwamna Bindow
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Sai dai sauran mutane biyu da su ka fafata da gwamnan, Mahmood Halilu Ahmed da tsohon shugaban hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribadu ba su amince da sakamakon zaben ba har ma sun bukaci uwar jam'iyyar ta soke zaben.

Wannan rikicin ya janyo cece-kuce tsakanin magoya bayan gwamna Bindow da kuma masu goyon bayan sauran 'yan takarar biyu.

A wata labari mai kama da wannan, Legit.ng ta kawo muku cewar har yanzu ana rikita-rikita kan wanda zai yi takarar Sanata na Yankin Kaduna ta Tsakiya a karkashin jam'iyyar APC duk da cewar anyi zaben fidda gwani a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel