APC na zolayar su Saraki da Atiku ya kayar a PDP a karshen mako

APC na zolayar su Saraki da Atiku ya kayar a PDP a karshen mako

- Karshen arewa kasa, inji APC da Saraki ya fadi zaben fidda gwani

- Wannan ya nuna delegates din PDP sun gaji da mulkin kama karya na shugaban majalisar

- Yakamata sanatoci ma su kwaikwaya ta hanyar tsige shi

APC na zolayar su Saraki da Atiku ya kayar a PDP a karshen mako

APC na zolayar su Saraki da Atiku ya kayar a PDP a karshen mako
Source: Twitter

Karshen alewa kasa, inji APC a yayin da Bukola Saraki ya fadi zaben fidda gwani na takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Jam'iyyar ta fadi haka ne ta bakin sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Yekini Nabena, inda yace delegates ma sun gaji da mulkin kama karya irin na shugaban majalisar.

"Quri'un tozarcin da Sanata Bukola Saraki ya samu a zaben fidda gwani sun kawo karshen burin shi na son kai da rashin gaskiya," inji jam'iyyar APC.

Mista Saraki, wanda bai dade da barin jam'iyyar APC zuwa PDP ba ya fito takarar neman shugabancin kasa amma sai yazo na uku a zaben fidda gwani da kuri'u 317,bayan Aminu Tambuwal mai kuri'u 693 da Atiku Abubakar mai kuri'u 1532.

Jam'iyya mai mulki tayi ta Kiran Saraki da ya sauka daga shugabancin majalisar tun bayan barin jam'iyyar da yayi amma tsohon gwamnan jihar Kwaran yayi biris dasu.

"Delegates din PDP sun nuna cewa sun gaji da mulkin kama karya irin na Saraki. Idan shugaba ya zamo ba abun yarda ba, baza'a dogara dashi ba kuma ba za'ayi yarjejeniya dashi ba, sai mutanen da yake mulka su canza shi da kuri'un su."

DUBA WANNAN: Albishirinku makarantaa jaridar NAIJ

Dole ne Saraki ya sauka daga kujerar mulkin majalisar. Bazai cigaba da zama shugaban masu rinjaye ba domin PDP ce mara rinjaye a majalisar.

"Sanatoci ma yakamata su kwaikwaya daga delegates ta hanyar tsige shi. Sabon shugaban majalisa wanda ba a zargi da wani aikin ta'addanci shi muke bukata"

Har yanzu dai mai magana da yawun Saraki bai maida martani ba.

Majalisar dattawa zata koma zama yau bayan da tayi satittika a kulle.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel