Hukumar 'Yan sanda ta cafke wani mai sayar da gurbatacciyar Barasa a jihar Legas

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wani mai sayar da gurbatacciyar Barasa a jihar Legas

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wani Matashi dan shekara 32 a duniya, Ifeanyi Udeh, ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda can jihar Legas bisa aikata babban laifi na sayar da gurbatacciyar barasa ga al'umma.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Edgal Imohimi, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Litinin yayin ganawarsa da manema labarai a babban birnin jihar na Ikeja.

Imohimi yake cewa, hukumar ta yiwa wannan matashi kwanton bauna yayin wani sintiri da jami'anta suka gudanar a unguwar Agbowa dake yankin Ikorodu na jihar.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wani mai sayar da gurbatacciyar Barasa a jihar Legas

Hukumar 'Yan sanda ta cafke wani mai sayar da gurbatacciyar Barasa a jihar Legas
Source: UGC

Babban jami'in dan sandan ya bayyana cewa, Udeh ya amsa laifin yayin da jami'an tsaro ke titsiye shi tare da cewa wannan gurbatacciyar barasa na da matukar lahani dake barazana ga lafiyar duk masu ta'ammali da ita.

KARANTA KUMA: Karancin ruwa da wuraren kiwo ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Tinubu

Kazalika hukumar 'yan sanda ta dakume wasuu Matasa biyu, Sulaiman Seun da Olamilekan Olaoluwa da suka shahara kan ta'addancin fashi da makami a unguwar Fashola dake yankin Sango-Ota a jihar Ogun.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani saurayi ya gurfana gaban kotu da laifin sauke kwazabarsa ta da namiji kan wata dattijuwa 'yar shekara 78 ta hanyar fyade a babban birnin Minna na jihar Legas.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel