Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere

Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar Yarbawa ta Afenifere na cikin ganawa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a yanzu haka.

Tawagar Afenifere karkashin jagorancin Ayo Adebanjo sun hada da Sanata Femi Okurounmu, Tokunbo Awolowo-Dosumu da sauransu.

Tawagar sun isa dakin karatun Olusegun Obasanjo, gidan Obasanjo na Abeokuta da misalin karfe 3:34 na rana.

Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere

Yanzu Yanzu: Obasanjo na ganawar sirri da Afenifere
Source: UGC

Kai tsaye dakin taron suka shige.

KU KARANTA KUMA: Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC

Duk kokari da akayi na jin tab akin daya daga cikin mambobin kungiyar Afenifere din kan dalilin zuwan nasu ya ci tura, yayinda aka shige dasu gidan da saukarsu wajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel