Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Aso Rock

Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Aso Rock

- 'Yan kungiyar Qadiriyyah sun ziyarci shugaba Buhari

- Mabiyar kungiyar 40 ne suka isa fadar shugaban kasa da ke Abuja karkashin jagorancin Sheikh Qaribullah S.N Kabara

- Wasu daga cikin 'yan fadar Buhari sun hallarci taron ciki har da gwaman Kano, Abdullahi Ganduje

Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Aso Rock

Shugabanin dariqar Qadiriyyah sun ziyarci Buhari a Aso Rock
Source: Twitter

A yau Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da 'yan kungiyar darikar Qadiriyyah a Fadar Aso Rock Villa da ke Abuja kamar yadda The Nation ta wallafa.

'Yan kungiyar wadda adadinsu ya kai 40 sun kaiwa shugaban kasar ziyara ne karkashin jagorancin Sheikh Qaribullah S.N Kabara.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Taron ya samu hallarci wasu daga cikin wadanda suka hallarci taron sun hada da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Ministan Sadarwa, Adebayo Shittu, Ministan Ilimi, Adamu Adamu da wasu daga cikin 'yan fadar shugaba Buhari.

A halin yanzu dai ba'a bayyana dalilin ziyarar na su ba.

A wani rahaton, Legit.ng ta kawo muku cewar gwamnan jihar Adamawa Bindow Jibrilla ya jadada goyon bayansa ga shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Jibrilla ya ce kasancewar tsohon shugaban kasa Atiku Abubakar dan asalin jihar Adamawa ba zai canja ra'ayin gwamnatinsa kan shugaba Buhari ba saboda irin ayyuka da ya shimfida musu a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel