Wani saurayi yayi ma tsohuwa yar shekara 78 fyade a wata jihar Arewa

Wani saurayi yayi ma tsohuwa yar shekara 78 fyade a wata jihar Arewa

Wata kotun majistare dake Minna tayi umurnin tsare wani manomi mai shekaru 32, Rilwanu Salisu a gidan yari bayan ya amsa laifin yiwa tsohuwa ýar shekara 78 fyade.

An gurfanar da Salisu ne akan fyade daidai da sashi 282 na kundin doka.

A cewar dan sanda mai kara, Mista Daniel Ikwoche, dan tsohuwar, Mukhtar Garba ne ya shigar da karar lamarin ga ofishin yan sandan Nasko a ranar 14 ga watan Satumba.

Ikwoche yace wanda ake zargin mazaunin kauyen Kwada a karamar hukumar Magama, ya shiga dakin tsohuwar, yayinda take bacci sannan ya haike mata inda ya sadu da ita ta karfin tsiya.

Wani saurayi yayi ma tsohuwa yar shekara 78 fyade a wata jihar Arewa

Wani saurayi yayi ma tsohuwa yar shekara 78 fyade a wata jihar Arewa
Source: UGC

Sannan kuma cewa ya jiwa tsohuwar rauni sosai inda jini ya balle mata.

Da aka karanto tuhumar da ake masa, ya amsa laifinsa inda ya roki kotu da tayi masa afuwa.

KU KARANTA KUMA: Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC

Sai dai babban alkalin kotun, Nasiru Muazu ya dakatar da rokon mai laifin saboda kotunsa bata da sauraron haka.

Muazu ya umurci yan sanda da su gabatar da kwafin takardar shariar zuwa daraktan doka na jihar don jin shawararsa.

Sannan yayi umurnin ci gaba da tsare mai laifin zuwa lokacin da za’a ji sakamokon shawarar nasa, sannan y adage zaman zuwa ranar 25 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel