Karancin ruwa da wuraren kiwo ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Tinubu

Karancin ruwa da wuraren kiwo ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Tinubu

Wani babban jigo kuma kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya kirayi gwamnatin tarayya akan ta gaggauta tanadar wuraren kiwo cikin yankunan kasar nan da ba a cin moriyar su a halin yanzu.

Tinubu cikin kiransa ya nemi gwamnatin tarayya akan ta maishe da yankunan kasar nan da ba a wani amfanar su a halin yanzu zuwa yankunan kiwo da a cewarsa hakan zai yi tasirin gaske wajen magance annoba ta rikicin makiyaya da manoma da ke ci gaba da ta'azzara.

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne cikin babban birnin kasar nan na Abuja yayin wani babban taro na kasa da aka gudanar kan samar da zaman lafiya mai dorewa kuma matabbaci.

A yayin taron da kafofin watsa labarai na The Nation da kuma gidan Talabijin na TV Continental suka dauki nauyin shiryawa, Tinubu ya ce dole sai gwamnatin tarayya ta yi hobbasa wajen tallafawa makiyaya da yankunan kiwo.

Karancin ruwa da wuraren kiwo ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Tinubu

Karancin ruwa da wuraren kiwo ya haddasa rikicin Makiyaya da Manoma - Tinubu
Source: Depositphotos

Tinubu wanda wani babban jigo na ma'aikatar sadarwa ta kasa ya wakilta a yayin taron, Sunday Dare ya bayyana cewa, sabanin jita-jitar kabilanci da kuma addini, rikicin makiya da manoma na aukuwa ta silar rashin wuraren kiwo da kuma karancin ruwan sha.

KARANTA KUMA: Jerin 'Yan Takarar Kujerar Shugaban Kasa da suka lashe Tikitin Jam'iyyun su

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana cewa, karancin wuraren kiwo a yankunan Arewa ya sanya Makiyaya ke nemawa dabbobin su mafaka a Kudandin kasar nan.

Cikin na sa jawaban a yayin taron, tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, Nuhu Ribadu, ya bayar da tabbacin sa na cewa rikicin makiyaya ba ya da nasaba ta kusa ko ta nesa da kasancewar shugaban kasa Muhammadu Buhari Bafulatani.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel