Tsuguni bata kare ba yayin da gwamnatin Buhari ta sanar da karancin albashin da za ta iya biyan ma’aikata

Tsuguni bata kare ba yayin da gwamnatin Buhari ta sanar da karancin albashin da za ta iya biyan ma’aikata

A yanzu haka tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta tsaya cak sakamakon matsayin da gwamnati ta tsaya akai na cewa lalai ba za ta iya biyan kudin da ya haura naira dubu ashirin da biyar a matsayin karancin albashi ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an dakatara da tattaunawar ne bayan gwamnati ta yi watsi da bukatar kungiyar kwadago duk da cewa kungiyar ta sauko daga naira dubu hamsin da shida zuwa naira dubu talatin, amma duk da haka gwamnati ta dage lallai sai naira dubu ashirin da biyar.

KU KARANTA: Barayin mutane sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mata 2 a Kaduna

Rahotanni sun tabbatar cewa da fari a yayin tattaunawar na ranar 4 ga watan Oktoba, gwamnati ta yi ma kungiyar kwadago tayin naira dubu ashirin da daya da dari bakwai ne (N21, 700) a matsayin sabon karancin albashi.

Sai dai kungiyar ta nuna rashin amincewarta da wannan tayi na gwamnati, inda ta ce gaskiya ba zata sabu ba, wai bindiga a ruwa, musamman duba da tsananin rayuwa tare da tashin farashin kayan abinci, daga na sai kungiyar kwadago ta sauki daga N56,000 zuwa N40,000.

Wannan rahoto na naira dubu asirin da biyar ya bayyana ne bayan kammala zaman tattaunawa tsakanin kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin tattauna da kungiyar kwadago, hakan ne ya sanya ma’aikata cikin zaman dar dar ganin cewa akan naira dubu arba’in aka cimma matsaya.

Dayake tsokaci game tattaunawar, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba ya ce nan bada jimawa bane gwamnatin tarayya za ta sanar da sabon karancin albashin da suka cimma matsaya, inda yace kwamitin ta kammala zamanta kuma ta mika ma shugaba Buhari rahotonta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel