Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC

Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya mayarwa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) martani akan ba’a da tayi game da rashin nasarar sa a zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 9 ga watan Oktoba yayi ba’a ga rashin nasarar Sarakin cewa “kudirinsa na zama shugaban kasa ya rushe.”

Don haka a wata sanarwa daga Yusuph Olaniyonu, babban hadiminsa a kafofin watsa labarai ya bayyana cewa APC zata ci gaba da jin faduwar gaba a duk lokacin da suka ji sunan Saraki.

Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC

Ku ji da matsalolin gabanku ba wai faduwa na a zaben fidda gwanin PDP ba – Saraki ga APC
Source: Depositphotos

Sannan Saraki ya shawarci jam’iyyar APC da shugabanta da su daina mayar da hankali kan lamuran jam’iyyar adawa sannan su nemi hanyar kawo karshen yakin basasa da ya barke a jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji sun kama shanaye da aka sace a Taraba

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnantin jihar Adamawa ta sake jadada goyon bayanta ga takarar shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2019 duk da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi nasara lashe tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.

Kwamishinan yadda labarai da tsare-tsare, Sajoh Ahmed ne ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba inda ya ce Buhari ya taka rawar gani a jihar Adamawa bayan darewarsa mulki, hakan yasa mutanen Adamawa ke goyon bayansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel