Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'

Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'

- Bayanai na ci gaba da bayyana kan gaskiyar yadda Atiku ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP

- Wani jigo na jam'iyyar PDP, ya ce Gwamna Aminu Tambuwal ne kowa ke tunain zai lashe zaben in banda goyon wasu jiga jigai da Atiku ya samu

- Yayin da Atiku ke son tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya zama mataimakinsa su kuwa kusoshin jam'iyyar PDP na sha'awar tsayar da Iweala

A zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP da ya gudana a babban filin wasanni na Adokiye Amiesimaka da ke garin Fatakwal, jihar Rivers, a karshen makon da ya gabata, Atiku ya kayar da 'yan takara 11 don zama dan takarar jam'iyyar a zabe na 2019.

Sai dai har zuwa yanzu, bayanai na ci gaba da bayyana kan yadda ya samu wannan nasara, musamman ganin cewa ya kara da jiga jigai a harkokin shugabancin kasar.

Wani jigo na jam'iyyar PDP, ya ce Gwamna Aminu Tambuwal ne kowa ke tunain zai lashe zaben in banda goyon bayan awanni 11 daga wasu janar-janar, da suka hada da Olusegun Obasanjo, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Theophilus Danjuma.

KARANTA WANNAN: Bayan kammala zaben fitar da gwani: INEC ta tattara adadin 'yan takara daga kowacce shiyya

Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'

Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'
Source: Twitter

Ya kara da cewa an sha daga sosai na juya ra'ayin Obasanjo, kasancewar ya sha alwashin ba zai goyawa Atiku baya a wannan zabe ba. Ya ce sai daga baya ne Obasanjo ya sauko tare da warware wannan alwashi da ya sha, biyo bayan matsin lambar da ya samu kusoshin kasar, da suka hada da wani tsohon shugaban wata babbar kasa a Duniya.

Wata majiyar kuma ta ce sai da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya tankwara gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike, da ya amince da sakamakon da kusoshin jam'iyyar suka yanke ba tare da turjiya ba.

Rahotanni sun kara bayyana cewa Atiku ya tsaya tsayin daka ga wadanda suka nuna masa goyon baya a Nigeria don ganin cewa ya samu tikitin takara a karkashin jam'iyyar. Sai dai, kakakin kungiyar yakin zaben Atiku, Segun Sowunmi ya yi ikirarin cewa babu wani sa hannun kusoshin jam'iyyar a wannan nasara ta Atiku.

KARANTA WANNAN: Kwanaki 2 da nasarar Atiku: Mutane 10,000 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a Niger Delta

Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'

Gaskiya ta tabbata kan yadda Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP bayan 'tsayin daka'
Source: Depositphotos

Dangane da Aminu Waziri Tambuwal kuwa, an masa alkawarin tikitin kujerar shugaban kasa a shekara ta 2013, sakamakon alkawarin da Atiku yayi na yin shugabanci a shekaru 4 kacal ba tare da neman tazarce ba. Haka zalika tuni dai har Tambuwal ya koma kujerar gwamnan jihar Sokoto a matsayin dan takarar kujerar karkashin PDP.

Tsohuwar ministar kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Farfesa Okonjo Iweal, ta kasance a sahun gaba daga cikin wadanda ake sa ran zata zama mataimakiyar Atiku. Yayin da shi Atiku ya ke son tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi ya zama mataimakinsa sabanin ra'ayin kusoshin jam'iyyar na sha'awar tsayar da Iweala.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel