Jiragen ruwa 13 jibge da kayayyaki sun dira Najeriya

Jiragen ruwa 13 jibge da kayayyaki sun dira Najeriya

Hukumar jiragen ruwan Najeriya NPA ta bayyana a yau Talata cewa Jiragen ruwa 13 dauke da kayayyaki daban-daban sun dira tashan jirgin ruwan Apapa da Tin Can dake jihar Legas

A jawabin tace bakwai daga cikin jiragen na dauke da man fetur, yayinda sauran shidan ke dauke da kwantenoni da takin gona.

A jiya, Hukumar jiragen ruwan Najeriya NPA ta alanta cewa jiragen ruwa 33 jibge da kayan man fetur, abinci, daga ranan 8 ga watan Oktoba zuwan ranan 27 ga wata. Hukumar ta ce ana sa ran zasu dira a tashoshin ruwan Apapa da Tincan dake jihar Legas.

KU KARANTA: Daga dawowa, Zanga-zanga ya barke majalisar dokokin tarayya

Hudu daga cikin jiragen 27 suna dauke da man fetur. Goma sha uku daga cikin jiragen na dauke kwantenoni, takin gona, kayayyakin mai. sauran na dauke da alkama, kifi, siga, karafuna.

Ministan man fetur, Ibe Kachikwu, ya jaddada cewa Najeriya zata fara tace danyen man fetirunta da kanta daga shekarar 2019.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel