2019: PDP na gab da rasa mambobinta da yawa a jihar Abia

2019: PDP na gab da rasa mambobinta da yawa a jihar Abia

Akwai wani shiri da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke yi na son sauya sheka zuwa wata jam’iyya a jihar Abi’a.

Wata kungiya a PDP ta bayyana cewa zasu dauki matakin komawa wata jam’iyya idan har ba’a magance abunda ta bayyana a matsayin fashi da tsakar rana da akayi lokacin zaben fidda gwani ba.

Jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani na ýan majalisar dokoki a Aba kuma dan asalin yankin Hon Blessing Nwagba ya fadi inda Hon Uzo Azubuike kwamishinan noma na jihar mai ci yayi nasara.

2019: PDP na gab da rasa mambobinta da yawa a jihar Abia

2019: PDP na gab da rasa mambobinta da yawa a jihar Abia
Source: Facebook

An tattaro cewa matasa a yankin sunyi zanga-zanga akan haka inda suka bayyana hakan a matsayin zamba cewa an basu dan takarar da ba zabin su bane.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya

Don haka sun umurci shugabannin jam’iyyar da su yi gaggawan daukar mataki ko kuma su kama gabansu su koma wata jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel