2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya

2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya

Wata kungiyar magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari mai suna Re-elect Buhari Movement (RBM), ta bayyana cewa billowar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019 alamu ne na cewa Shugaban kasar ya ci zabe ya gama.

Da suke taya Shugaban kasar murna gabannin zaben, kungiyar a wata sanarwa ta hannun shugabanta, Emmanuel Umohinyang, tayi ikirarin cea Shugaba Buhari zai lallasa Atiku ba da wasa ba a zabe mai zuwa.

2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya

2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya
Source: Twitter

Sun kara da cewa bayyanar shugaba Buhari shi kadai a matsayin da takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zabe mai zuwa ya samo asali ne saboda namijin kokarin da yayi a shekaru uku da yayi kan mulki.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da kowani shafi a dandalin sada zumunta - IBB

A cewar kungiyar, shugaban kasar ya cika alkawarin day a dauka ta hanyar kafa muhimman shiri cikin shekaru uku.

A halin da akeciki, Legit.ng ta rahoto cewa a kokarin PDP, na ganin ta kwato mulki daga hannun gwamnatin APC a watan Fabrairu, an fara baiwa tsohon mataimakin Obasanjo shawarar wanda ya kamata ya dauka a matsayin na biyu a takararsu, inda hankulla suka rabu biyu kacokan.

A yanzu ko a cikin kabilar Ibo, masu kokarin sun kawo koda kujerar mataimaki ne a badi, ra'ayi ya rabu biyu, inda wasunsu ke ganin ya kamata Atikun ya dauko Dr. Okwesilieze Nwodo, wasu kuwa ke ganin Okonjo Iweala ya kamata ya dauko don a farantawa Obasanjo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel