Adamawa ta Buhari ce duk da cewa Atiku yana takara - Gwamna Jibrilla

Adamawa ta Buhari ce duk da cewa Atiku yana takara - Gwamna Jibrilla

- Kwamishinan yada labarai da tsare-tsare na jihar Adamawa, Sajoh Ahmed ya ce shugana Buhari ya yiwa al'ummar jihar Adawama ayyuka da dama tun bayan darewarsa mulki

- Ahmed ya ce goyon bayan da gwamna Jibrilla ke bawa Buhari ba za ta canja ba saboda kasancewar Atiku dan takarar shugabancin kasa na PDP

- Ya ce har yanzu jihar Adamawa na goyon bayan shugba Muhammadu Buhari 100%

Gwamnantin jihar Adamawa ta sake jadada goyon bayanta ga takarar shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2019 duk da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi nasara lashe tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.

Adamawa ta Buhari ce duk da Atiku yana takara - Gwamna Jibrilla

Adamawa ta Buhari ce duk da Atiku yana takara - Gwamna Jibrilla
Source: Twitter

Kwamishinan yadda labarai da tsare-tsare, Sajoh Ahmed ne ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 8 ga watan Oktoba inda ya ce Buhari ya taka rawar gani a jihar Adamawa bayan darewarsa mulki, hakan yasa mutanen Adamawa ke goyon bayansa.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin wasu jiga-jigan 'yan siyasa 10 da ba za su koma majalisa ba

Duk da ya ke Kwamishinan bai ambaci suna Atiku a zahiri ba, ya ce ne kasancewar dan siyasar jihar Adamawa ya lashe zaben tikitin takarar shugabancin kasa a wata babban jam'iyya gagarumin lamari ne.

Sai dai Ahmed din ya ce gwamna Jibrilla yana da dan takararsa kuma a ko yaushe za su zabi zahiri a maimakon alkawurran da babu tabbas din za'a cika musu.

A wata labarin, Legit.ng ta kawo muku cewar dan takarar na PDP, Atiku Abubakar ya mayar da martani ga shugaba Muhammadu Buhari inda ya ce ba gaskiya bane cewar ya yi amfani da kudi wajen samun nasara a zaben fidda gwani na PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel