Abubuwa 3 da ake da ake sa rai a yanzu da majalisar dokokin kasar suka dawo

Abubuwa 3 da ake da ake sa rai a yanzu da majalisar dokokin kasar suka dawo

A yau Talata, 9 ga watan Oktoba ne majalisar dokokin kasar ta dawo bakin aiki bayan dogon hutun da ta tafi a ranar 24 ga watan Yuli.

Majalisar dokokin kasar ta tafi hutun shekara a ranar 24 ga watan Yuli bayan yawan sauye-sauyen sheka da aka samu da kuma shirye-shiryen zaben fidda gwanaye na jam’iyyun siyasa.

Don haka a yanzu da majalisar ta dawo zama akwai muhimman abubuwa da ake sanya ran zata aiwatar bayan afkuwar lamura da dama a kasar.

Abubuwa 3 da ake da ake sa ran za su faru a yanzu da majalisar dokokin kasar ta dawo daga hutu

Abubuwa 3 da ake da ake sa ran za su faru a yanzu da majalisar dokokin kasar ta dawo daga hutu
Source: Depositphotos

Daga cikinsu akai:

1. Dokar zabe

Dokar zabe shine batu na farko kuma mafi muhimmanci da ake ganin majalisar zata zanta a kai sannan da kuma duba batun kasafin kudin hukumar zaben kasar INEC.

2. Batun amso basussuka

Abu na biyu da ake sanya ran majalisar zata yi duba akai shine batun duba basussukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke neman majalisar ta amince.

3. Lamarin sauya shekar shugabannin majalisar dokokin

Haka zalika ana sa ran majalisa zata dauki matakin sauya shugabannin majalisun guda biyu wato na dattawa da wakilai, inda ake ganin zasu nemi tsige Bukola Saraki da Yakubu dogara daga matsayinsu biyo bayan komawarsu jam’iyyar PDP mai adawa a kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta dawo bayan dogon hutu

An shirya dawowa zama a ranar 25 ga watan Satumba, amma aka dage zua ranar 9 ga watan Oktoba saboda zabukan fidda gwanaye na jam’iyyun siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel