Jerin 'Yan Takarar Kujerar Shugaban Kasa da suka lashe Tikitin Jam'iyyun su

Jerin 'Yan Takarar Kujerar Shugaban Kasa da suka lashe Tikitin Jam'iyyun su

Rahotanni sun bayyana cewa, ko shakka ba bu guguwar siyasa ta mamaye duk wani lungu da sako na kasar nan sakamakon zabukan fidda gwanayen takarar kujeru daban-daban na jam'iyyu da aka gudanar makonni kadan da suka shude.

A sanadiyar haka ya sanya yau shafin jaridar Legit.ng ya kawo muku jerin gwanayen takara na jam'iyyun siyasa daban-daban da za su fafata takara ta hankoron kujerar shugaban kasa a yayin babban zaben na 2019.

Shugaba Buhari yayin mallakar takardun bayyana kudirin takara na jam'iyyar sa ta APC

Shugaba Buhari yayin mallakar takardun bayyana kudirin takara na jam'iyyar sa ta APC
Source: Depositphotos

Kamar yadda rahotanni da sanadin kafofin watsa labarai suka ruwaito musamman jaridar The Nation, Pulse da kuma Premium Times, mun kawo muku jerin sunayen gwanayen takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyu daban-daban da za su fafata a ranar 14 ga watan Fabrairun 2019.

Ga jerin masu hankoron kujerar shugaban kasar tare da jam'iyyu da za su rikewa tutoci a yayin zaben kamar haka:

1. Muhammadu Buhari - Jam'iyyar APC

2. Atiku Abubakar - Jam'iyyar PDP

3. Janar John Ogbor - Jam'iyyar APGA

4. Yabagi Yusuf Sani - Jam'iyyar ADP

5. Fasto Habu Aminchi - Jam'iyyar PDM

6. Mista Chuks Nwakachukwu - Jam'iyyar AGA

7. Donald Duke - Jam'iyyar SDP

8. Omoyele Oyesore - Jam'iyyar AAC

9. Fela Durotoye - Jam'iyyar ANN

10. Tope Fasua - Jam'iyyar ANRP

KARANTA KUMA: Kada wanda ya fara yakin neman zabe yanzu - INEC ta gargadi 'Yan takara da Jam'iyyu

11. Obiageli Ezekwesili - Jam'iyyar ACPN

12. Kingsley Moghalu - Jam'iyyar YPP

13. Eunice Atuejide - Jam'iyyar NIP

14. Olusegun Mimiko - Jam'iyyar ZLP

15. Adesina Fagbenro-Byron - Jam'iyyar KP

16. Chike Ukaegbu - Jam'iyyar AAP

17. Hamza Al-Mustapha - Jam'iyyar PPN

18. Alistair Soyode - Jam'iyyar YES

19. Obadiah Mailafia - Jam'iyyar ADC

20. Ahmed Buhari - Jam'iyyar SNP

21. Usman Ibrahim Alhaji - Jam'iyyar NRM

22. Eniola Ojajuni - Jam'iyyar AD

23. Gbenga Olawepo Hashim - Jam'iyyar APT

24. Edozie Madu - Jam'iyyar ID

25. Williams Awosola - Jam'iyyar DPC

26. Habu Aminchi - Jam'iyyar PDM

27. Moses Shipi - Jam'iyyar ABP

28. Peter Nwangwu - Jam'iyyar WTPN

29. Rabia Cenzig - Jam'iyyar NAC

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, jiragen ruwa 13 jibge da kayayyaki sun iso tashar jirgin ruwa ta Apapa da Tin Can can jihar Legas a Kudancin Najeriya.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel