Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta dawo bayan dogon hutu

Yanzu Yanzu: Majalisar dokoki ta dawo bayan dogon hutu

Majalisar dokokin kasar ta dawo bakin aiki a ranar Talata, 9 ga watan Oktoba bayan dogon hutun da ta tafi a ranar 24 ga watan Yuli, 2018.

Mafi akasarin ýan majalisan basu hallara ba yayinda aka lura da shiru da karancin mutane a majalisar dokokin kasar.

Haka zalika an tsaurara matakan tsaro a majalisar dokokin kasar yayinda aka gano jami’ai da motocin yan sanda da dama a haraban wajen.

An gano wasu jami’an tsaro kuma wanda inifam dinsu bai bayyana ko su wanene ba tare da umurnin kada su bari wadanda ba manyan mutane ba shiga majalisar.

Majalisar dokokin kasar ta tafi hutun shekara a ranar 24 ga watan Yuli bayan yawan suye-sauyen sheka da aka samu da kuma shirye-shiryen zaben fidda gwanaye na jam’iyyun siyasa.

KU KARANTA KUMA: Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira

An shirya dawowa zama a ranar 25 ga watan Satumba, amma aka dage zua ranar 9 ga watan Oktoba saboda zabukan fidda gwanaye na jam’iyyun siyasa.

Kafin hutun akwai lamura da suke gaban majalisar wanda suka hada da amincewa da kasafin kudin 2018 da na zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel