PDP 2019: Wanda zai marawa Atiku a 2019 ya raba kan manyan kasar nan

PDP 2019: Wanda zai marawa Atiku a 2019 ya raba kan manyan kasar nan

- Atiku Abubakar ne zai kara da Buhari nan da wata 5

- Ana sa rai Atiku zai dauko mataimaki daga yankin kudu maso gabas

- Wasu na ganin akwai inda ya kamata yaje neman mataimaki

PDP 2019: Wanda zai marawa Atiku a 2019 ya raba kan manyan kasar nan

PDP 2019: Wanda zai marawa Atiku a 2019 ya raba kan manyan kasar nan
Source: UGC

A kokarin PDP, na ganin ta kwato mulki daga hannun gwamnatin APC a watan Fabrairu, an fara baiwa tsohon mataimakin Obasanjo shawarar wanda ya kamata ya dauka a matsayin na biyu a takararsu, inda hankulla suka rabu biyu kacokan.

A yanzu ko a cikin kabilar Ibo, masu kokarin sun kawo koda kujerar mataimaki ne a badi, ra'ayi ya rabu biyu, inda wasunsu ke ganin ya kamata Atikun ya dauko Dr. Okwesilieze Nwodo, wasu kuwa ke ganin Okonjo Iweala ya kamata ya dauko don a farantawa Obasanjo.

DUBA WANNAN: Yadda Kwankwaso zai koyi siyasa a hannun Tinubu

Manyan yankin, na son Atiku ne saboda yayi akawarin sauya wa jam'iyyar da ma Najeriya akala, inda zai sauya yadda ake rabon arzikin kasa, kowa tashi ta fisshe shi, wanda zai kara talauta yankunan da basu da wani arziki sai yawan almajirai.

Bangarorin da ke kokarin fadi aji, akwai na 'yan Neja Delta, akwai na yan kabilar Ibo, akwai bangaren shugaban jam'iyya, akwai kuma na shugaban kamfe na Atikun, Emmanuel Iwuanyanwu, wanda suma ke son suce su suka bada mataimaki.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel