Ba ni da kowani shafi a dandalin sada zumunta - IBB

Ba ni da kowani shafi a dandalin sada zumunta - IBB

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ya nisanta kansa daga dukkanin shafukan zumunta da aka bude da sunansa.

A wata sanarwa daga ofishin labaransa, Babangida wanda aka fi sani da IBB, ya ce shafukan twitter dake watsa jawabai da sunansa ba nasa bane.

Hakan ya biyo bayan wani sakon taya murna ga Atiku Abubakar wanda yayi nasarar zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a karshen mako.

Ba ni da kowani shafi a dandalin sada zumunta - IBB

Ba ni da kowani shafi a dandalin sada zumunta - IBB
Source: Depositphotos

An wallafa sakon ne da sunan tsohon shugaban kasar, inda ya jadadda cewa shi bashi ne ya wallafa wannan sako ba sannan kuma cewa wannan shafi ba nasa bane domin shi baya ko daya daga cikin shafukan zumunta.

KU KARANTA KUMA: Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus

Daga karsheyayi kira ga jama'a da su hankalta da irin shafukan bogi da suka cike dandalin zumunta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel