Wani da ake tuhuma da damfarar Janar din Soja ya shiga hannu

Wani da ake tuhuma da damfarar Janar din Soja ya shiga hannu

- An gurfanar da wani Mohammed Sanni Zubair da ake zargin dan damfara ne a gaban kotu

- Ana tuhumar Zubair da yiwa EFCC karya tare da yaudarar wani tsohon Janar din soja inda ya yi masa awon gaba da N180 miliyan

- Zubair ya musanta aikata laifin hakan yasa kotu da dage cigaba da sauraon shari'ar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba

A jiya Litinin 8 ga watan Oktober ne hukumar yaki rashawa na EFCC ta gurfanar da wani Mohammed Sanni Zubair a babban kotun tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja bisa aikata laifuka 4 masu alaka da damfara da zamba.

Zubair da ya dade yana damfarar mutane inda aka bayyana cewar yana aiki ne tare da wasu kungiya da suka kware wajen damfarar mutane.

Wani da ake tuhuma da damfarar Janar din Soja ya shiga hannu

Wani da ake tuhuma da damfarar Janar din Soja ya shiga hannu
Source: Twitter

Asirin Zubairu ya tonu ne bayan daya daga cikin yaran Manjo Janar Geofferey Ejiga (murabus) ya shigar da karar ofishin EFCC inda ya ce wasu 'yan damfara sun yaudari mahaifinsa sun sace masa kudi fiye da N180 miliyan.

DUBA WANNAN: Adamawa ta Buhari ce duk da cewa Atiku yana takara - Gwamna Jibrilla

Bincike ya nuna cewa an taba EFCC ta taba kama Zubair a 2016 bisa laifin damfara inda ya amsa laifinsa a lokacin amma ya ce wani Johnson Abiodun wanda aka gano asalin sunansa Nuhu Kasim ne ya ke daukan nauyinsa.

EFFC ta shigar da Zubair kara a kotu bisa tuhumarsa da yiwa wani jami'in hukumar mai suna Naziru Aminu Shehu karya a watan Oktoban 2016 yayin da ya ke aiki a Abuja wanda hakan ya sabawa sashi na 39(2) (a) da (b) na dokar EFCC ta 2004.

Sai dai wanda ake tuhumar bai amince da aikata laifin ba.

An Zubair kana Alkalin kotun da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel