Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira

Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira

- Yan sanda sun cafke mutane biyar dake siyar da naira

- Hakan ya biyo bayan sabn dokar da babban bankin Najeriya ta kafa akan masu siyar da kudin kasar

- An kama mutanen ne a jihar Ondo

Rundunar yan sanda a jihar Ondo sun kama mutane biyar akan zargin siyar da kudin kasar wato naira.

A cewar kakakin yan sandan jihar Ondo, Mista Femi Joseph yan sanda dake aiki tare da babban bankin kasar (CBN) sun kama masu laifin ne a ranar Alhamis da Juma’a da suka gabata.

Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira

Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira
Source: Depositphotos

A cewar Joseph wannan aiki na son yin maganin masu siyar da Naira duk da gargadin da ýan sanda da CBN suka sha yi masu.

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa wadanda aka kama sun hada da maza da mata a yankunan jihar daban-daban a lokacin da aka kai mamayar dauke da kudade da yawa.

KU KARANTA KUMA: Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus

Tuni dai aka fara gudanar da binkice kan lamarin don gano yadda aka samo sabbin kudaden, inji Joseph.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel