Kada wanda ya fara yakin neman zabe yanzu - INEC ta gargadi 'Yan takara da Jam'iyyu

Kada wanda ya fara yakin neman zabe yanzu - INEC ta gargadi 'Yan takara da Jam'iyyu

Hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta yi shimfidar wani gagarumin takunkumi na gargadin dukkanin jam'iyyu da 'yan siyasar kasar nan kan hana su fara gudanar da duk wani nau'in yakin neman zabe kafin lokacin lokacin da doka ta shar'anta.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shine ya bayyana hakan yayin wani taro na kwararru da masana harkokin zabe da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na Abuja a ranar Litinin din da ta gabata.

Farfesa Yakubu ya tunatar da jam'iyyu da kuma 'yan takara na siyasar kasar nan dangane da tanadin sashe na 99 da ya haramata duk wani nau'in gudanar da yakin neman zaben kwanaki 90 kafin gudanarsa.

Dangane da tanadi na jadawalin hukumar INEC, manema takarar kujerar shugaban kasa da kuma majalisun tarayya za su fara gudanar da yakin neman zabe a ranar 18 ga watan Nuwamba yayin da ta kayyade ranar 1 ga watan Dasumba ga manema takarar kujerar gwamna da kuma 'yan majalisun dokoki na jihohi.

Kada wanda ya fara yakin neman zabe yanzu - INEC ta gargadi 'Yan takara da Jam'iyyu

Kada wanda ya fara yakin neman zabe yanzu - INEC ta gargadi 'Yan takara da Jam'iyyu
Source: Facebook

Kamar yadda shafin jaridar Premium Times ya ruwaito, Farfesa Yakubu ya gargadin 'yan takara da kuma dukkanin jam'iyyun siyasa na kasar nan akan tabbatar da kiyaye wannan doka ta hanyar yiwa jadawalin ta biyayya.

KARANTA KUMA: Zaben Fidda Gwani: 'Dan Majalisar Wakilai ya lallasa 'Dan uwansa wajen lashe tikitin takara na jam'iyyar PDP a jihar Kano

Kazalika shugaban hukumar ya kayyade ranakun gabatar da sunayen dukkanin 'yan takara da suka lashe tikitin jam'iyyun su na kujeru daban-daban yayin zaben fidda gwanaye da aka gudanar makonni kadan da suka shude.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, gwamnan jihar Adamawa, Muhammad Jibrilla Bindow, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan Atiku Abubakar ba, tsohon mataimakin shugaban kasa da ya lashe tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP.

Na nan tafe, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika muna mika godiyar mu ta musamman a gare ku yayin da kuke ci gaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel