Barayin mutane sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mata 2 a Kaduna

Barayin mutane sun kashe mutum daya, sun yi garkuwa da mata 2 a Kaduna

Wasu gungun yan bindiga sun halaka wani matashi tare da yin awon gaba da wasu mata biyu a kamar hukumar Birnin Gwari na jahar Kaduna, garin da ya dade yana fama da ayyukan barayin mutane, inji rahton jaridar daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin a layin mahuta cikin unguwar Tabanni dake garin Birnin Gwari, inda masu garkuwa da mutanen suka kashe Ado Tabanni.

KU KARANTA: Yadda wasu yan fashi da makami suka yi ma jami’in Dansanda kisan gilla a Kalaba

Yan bindigan sun kashe Ado Tabanni mahaifin wani ma’aikacin kiwon lafiya wanda yayi murabus, Lawal Ado, sa’annan suka yi awon gaba da matarsa da matar makwabcinsa, duk a layin Mahuta.

Sai dai rahoton ya bayyana cewa rundunar Yansandan jahar Kaduna bata ce uffan ba game da lamarin har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, domin kuwa duk kokarin majiyarmu ta yi na jin ta bakin kaakakin yansandan jahar, Mukhtar ya ci tura.

Idan ba yanzu ba da lamarin ya dan lafa ba, karamar hukumar Birnin Gwani ta yi fama da ayyukan yan bindiga da na masu garkuwa da mutane, inda suka dinga cin karensu babu babbaka, wanda hakan ya janyo asarar dimbin dukiya da rayukan jama’a da dama.

A wani lokaci yan bindigan sun kai ga tawagar yan rakiya amarya a lokacin ake kan hanyar raka wata amarya gidanta a daren da aka daura mata aure, inda suka yi garkuwa da amaryar tare da kashe jama’a da dama. Haka zalika yan bindigan sun sha kashe jami’an tsaro ciki har da Sojoji.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel