Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus

Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus

- Uche Secondus ya bayyana cewa billowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar ya nuna cewa PDP ta dauki hanyar zuwa Villa

- Shugaban PDP din ya ce sunyi taronsu cikin kwanciyar hankali sabanin yadda ake ta hasashe

- Ya kuma mika godiya ga mambobin jam'iyyar a fadin kasar

Shugaban jam’iyyar People's Democratic Party (PDP) na kasa, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa billowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar ya nuna cewa PDP ta dauki hanyar zuwa fadar shugaban kasa, wato Aso Villa cikin sauri.

Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus

Atiku: Babu shakka PDP ta dauki hanyar zuwa Villa - Secondus
Source: Twitter

Cif Secondus, a wata sanarwa day a saki a jiya, Litinin 8 ga watan Oktoba ta hannun hadminsa, Mista Ike Abonyi, ya kuma nuna godiya ga mambobin jam’iyyar a fadin kasar da kuma na kasashen waje bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin an gudanar da babban taron jam’iyyar cikin nasara.

A ranar Asabar da Lahadi da suka gabata ne jam’iyyar tayi babban taron ta na kasa a Port Harcourt.

KU KARANTA KUMA: Sanatoci sun yi zaman musamman na kokarin tsige Saraki a Majalisa

Jigon PDP din yace an kunyata duk wadanda ke ta has ashen cewa za’a gama taron cikin rikici da tashin hankali ne.

Inda ya jadadda cewa an samu zaman lafiya da hadin kai sosai a jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel