Sanatoci sun yi zaman musamman na kokarin tsige Saraki a Majalisa

Sanatoci sun yi zaman musamman na kokarin tsige Saraki a Majalisa

Mun samu labari cewa ‘Yan Majalisar Jam’iyyar APC mai mulki sun shiga wani taro na musamman cikin dare domin ganin yadda za a kitsa tsige Shugaban Majalisar Dattawa watau Bukola Saraki.

Sanatoci sun yi zaman musamman na kokarin tsige Saraki a Majalisa

'Yan Majalisan APC na kokarin sauke Saraki daga kujerar sa
Source: Depositphotos

Daily Trust ta rahoto cewa Sanatocin APC sun gana a wani wuri a boye a Birnin Tarayya Abuja cikin dare jiya domin tsige Bukola Saraki daga kujerar sa. Yanzu dai Saraki ya sauya sheka inda ya bar Jam’iyyar APC mai rinjaye zuwa PDP.

A yau Talata ne dai da aka sa rai Majalisa za ta dawo aiki bayan wani dogon hutu na kusan watanni 2. Yanzu mun ji cewa an dage zaman zuwa gobe domin yin makokin wani ‘Dan Majalisar Wakilai da ya rasu makonni biyu da su ka wuce.

Ana dai tunani idan Majalisa ta gama jimamin Marigayi Honarabul Funke Adedoyin za ta fara neman yadda za a tunbuke Bukola Saraki. Sanata Biodun Olujimi ta Jam’iyyar adawa ta PDP dai ta nuna cewa sam hakan ba za ta sabu ba a Majalisar.

KU KARANTA: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar a PDP

A karshen Yuli ne Saraki ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP wanda ya sa wasu ‘Yan Majalisa da manyan APC su kace dole ya bar kujerar sa. Wani Sanatan APC dai ya nuna cewa zai yi wahala a iya sauke Saraki.

Wasu ‘Yan Majalisar dai sun bayyanawa Majiyar ta mu cewa da-kamar wuya a iya canza shugabancin Majalisa domin kuwa APC ta batawa ‘Ya ‘yan ta rai wajen zaben fitar da gwani. PDP maras rinjaye ce dai yanzu ke rike da Majalisa.

Labari dai na zuwa mana cewa Atiku Abubakar wanda yayi nasara a zaben kujerar Shugaban kasa na PDP dai ya fara kokarin ceton Saraki da Yakubu Dogara a Majalisar Tarayyar Najeriyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel