Shugaba Buhari zai tattara kayan sa ya koma Daura a 2019 inji Dino Melaye

Shugaba Buhari zai tattara kayan sa ya koma Daura a 2019 inji Dino Melaye

Sanata Dino Melaye wanda yake wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa ya fito tofa albarkacin bakin sa game da 2019 ya bayyana wanda zai lashe zaben 2019 tsakanin Atiku da Shugaba Buhari.

Shugaba Buhari zai tattara kayan sa ya koma Daura a 2019 inji Dino Melaye

Sanatan Kogi Dino Melaye yace Buhari zai koma gida a 2019
Source: Instagram

Dino Melaye wanda ya saba jawo abin magana yayi amfani da kafar sadarwa na Instagram wannan karo inda ya nuna cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben Shugaban kasa na 2019.

Sanatan na PDP ya bayyana cewa haka-zalika Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lallaba ya koma Daura inda nan ne Garin sa bayan zaben 2019 domin zai sha kayi. Sanatan ya bayyana wannan ne duk a makon nan.

KU KARANTA: Gwamnan Gombe ya taya Atiku murna bayan ya ci zabe a PDP

‘Dan Majalisar wanda ya bar Jam’iyyar APC kwanaki ya marawa Bukola Saraki ne a zaben fitar da gwani na PDP da aka yi kwanan nan kamar yadda mu ka samu labari. Sai dai yanzu Sanatan yace Atiku zai yi nasara a badi.

Yayin da ake batun Atiku Abubakar, jiya kun ji cewa Dino Melaye na iya rasa kujerar sa a Majalisar Dattawa domin zai gwabza ne da wani tsohon Sanatan da yayi fice a Kogi a APC watau Smart Adeyami a zaben 2019.

Wasu dai na ganin akwai datti a kan Atiku Abubakar don haka ba zai kai labari ba a zaben 2019. Shi dai Dino Melaye yace ba shakka Shugaba Buhari zai hau mota a titi ya koma Daura a shekarar badi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel