Wani gwamna da ya sha kayi a hannun Atiku ya koma jaharsa don tsayawa takarar gwamna

Wani gwamna da ya sha kayi a hannun Atiku ya koma jaharsa don tsayawa takarar gwamna

Jam’iyyar PDP reshen jahar Sakkwato ta sanar da sauya dan takararta na gwamnan jahar Sakkwato Alhaji Mannir Dan Iya da sunan gwamnan jahar kuma dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP da ya sha kayi a hannun Atiku Abubar zaben fidda gwani, Aminu Waziri Tambuwal.

Sai dai bayan kammala zaben ne sai kallo ya koma sama, inda dan takarar da ake zaton nada goyon bayan jigon jam’iyyar PDP kuma gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike, wato Aminu Waziri Tambuwl ya sha kayi bayan ya samu kuri’u 693, yayin da Atiku mai karfin arziki ya lashe zaben da kuri’u 1, 532.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jam’iyyar ta aika da sunan Tambuwal ne don ya maye gurbin kwamishinan kula kananan hukomomin jahar Sakkwato, Manir Dan Iya wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da zai tsaya mata takarar gwamna a 2019.

Wani gwamna da ya sha kayi a hannun Atiku ya koma jaharsa don tsayawa takarar gwamna

Tambuwal
Source: UGC

An tabbatar da takarar ta Tambuwal ce a daren Lahadi 7 ga watan Oktoba, inda wakilan jam’yyar watay daliget daga kananan hukumomin jahar 23 suka taru a babban ofishin jam’iyyar PDP dake garin Sakkwato, inda suka bayyan goyon bayansu ga Tambuwal.

Biyo bayan bayyana bukatarsu ga uwar jam’iyyar, nan da nan ba tare da bata lokaci ba, Mannir Dan Iya ya amince ya janye takararsa don baiwa Tambuwal damar neman tazarce a kujerar gwamnan jahar Sakkwato, kuma ya sanar da haka da yan jam’iyyar.

Amma wani abu mai daure kai shine da aka tambayi shugaban jam’iyyar PDP na sakkwato, Ibrahim Milgoma game da wannan batu sai yace “Mun tara daliget ne don mu gode musu bisa goyon bayan da suka bamu a yayin gudanar da zabukan fidda yan takarkaru.

“Ba mun tarasu bane don tabbatar da takarar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, tunda muna dan takararmu tun tuni, kuma shine Mannir Dan Iya, bamu canza shi da kowa ba.” Inji shi.

sai dai wasu manazarta al’amuran siyasar Najeriya na ganin wannan mataki a matsayin shiri ne tun daga farko, inda suke ganin dama can gwamnan jahar ta nemi kwamishinannasa ta tsaya ne don rike masa tikitin domin koda ya fadi takarar fidda gwani na shugaban kasa a PDP, sai ya dawo ya amshi abinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel