2019: PDP ta fadawa INEC kar bankara dokar kasa a Zamfara saboda APC

2019: PDP ta fadawa INEC kar bankara dokar kasa a Zamfara saboda APC

Babbar Jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta gargadi Hukumar zabe na kasa watau INEC da cewa kar ta bankara dokar ta wajen karbar sunayen ‘Yan takaran Jam’iyyar APC daga Jihar Zamfara.

2019: PDP ta fadawa INEC kar bankara dokar kasa a Zamfara saboda APC

An nemi INEC ta guji cusa 'Yan takaran APC a Zamfara
Source: Depositphotos

Jam’iyyar PDP ta tunawa Hukumar zabe cewa Ranar Lahadi ne ranar karshen da aka ware domin karbar sunayen ‘Yan takara daga Jam’iyyun kasar. Sai dai har wannan wa’adi ya kare PDP tana zargin APC ba ta da ‘Yan takara a Zamfara.

Sakataren yada labarai na Jam’iyyar PDP watau Kola Ologbondiyan ya fitar da jawabi a Garin Abuja a jiya da dare inda yake cewa Hukumar zabe na neman yi wa Jam’iyyar APC mai mulki yadda ta ke so wanda ya sabawa dokar kasa.

KU KARANTA: Manyan badakaloli 5 da Atiku ya tafka - Rahoton Amurka

Kola Ologbondiyan ya zargi wasu manyan Jami’an Hukumar zabe da ganawa da manyan APC wajen kokarin cusa sunayen ‘Yan takaran APC a Jihar duk da Jam’iyyar ta gaza cin ma sharudn da aka gindaya na shiga takara a zaben 2019.

Jam’iyyar PDP dai tace ba za ta amince da wannan yunkuri da ake yi ba inda ta bayyana cewa APC ta jefa kan ta cikin matsala a dalilin gaza gudanar da zabukan fitar da gwani a kan kari

Shekaran jiya ne dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki ‘Yan APC da cewa su yi zaman su a Jam’iyyar ko da sun fadi zaben fitar da gwanin da aka gudanar kwanakin da su ka wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel