Dankwambo ya amince da shan kayi a hannun Atiku: Ya bayyana makomarsa a PDP

Dankwambo ya amince da shan kayi a hannun Atiku: Ya bayyana makomarsa a PDP

Gwamnan jihar Gombe, kuma daya daga cikin wadanda suka yi takarar kujerar shugaban kasar Nigeria karkashin jam'iyyar APC, Ibrahim Dankwambo, ya yi jawabi a karon farko bayan da ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar da ya gudana a Fatakwal, jihar Rivers.

Dankwambo ya sha kayi ne a zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa, karkashin PDP a hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Atiku ya samu kuri'u 1532 yayin da Dankwambo ya samu kuri'u 111 kacal.

KARANTA WANNAN: Kamanceceniya 5 dake a tsakanin Shugaba Buhari da Atiku Author: Mustapha Saddiq

Dankwambo ya amince da shan kayi a hannun Atiku: Ya bayyana makomarsa a PDP

Dankwambo ya amince da shan kayi a hannun Atiku: Ya bayyana makomarsa a PDP
Source: Twitter

Da ya ke bayyana amincewa da shan kayi a zaben, gwamnan yayin da ya ke taya Atiku murnar wannan nasarar a shafinsa na Twittter, ya sha Alwashin aiki kafada-da-kafada da Atiku don tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ta lashe zaben 2019.

Ya rubuta cewa, "Ina taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar murnar zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyarmu mai albarka PDP.

"Hakika kanmu a hade yake karkashin inuwa daya kuma zamu yi aiki tukuru don ganin cewa jam'iyyarmu ta samu nasara a babban zaben 2019."

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel