Tsohon IG da APC ta hana takara ya jagoranci addu'ar Allah-tsine a hedkwatar jam'iyya

Tsohon IG da APC ta hana takara ya jagoranci addu'ar Allah-tsine a hedkwatar jam'iyya

Tsohon shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, Suleiman Abba, da APC ta haramtawa takarar neman kujerar Sanatan jihar Jigawa ta tsakiya ya ziyarci hedkwatar jam'iyyar a yau, Litinin.

Abba ya bawa mutane da dama mamaki bayan ya jagoranci wata doguwar addu'a ta yin tofin ala-tsine ga duk masu hannun cikin haramta masa yin takara a jam'iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewar Abba ya ziyarci hedkwatar ta APC ne domin bayyana rashin jin dadinsa bisa rashin amincewa da takarar sa da jam'iyyar ta yi.

Da yake magana da manema labarai bayan bayyana rashin jin dadinsa ga shugabannin jam'iyyar, Abba ya yi addu'ar Allah ya kawar da duk mai hannu cikin hana shi takara daga ofis domin burinsu na lalata kima da martabar APC ne.

Tsohon IG da APC ta hana takara ya jagoranci addu'ar Allah-tsine a hedkwatar jam'iyya

Tsohon IG Suleiman Abba
Source: Twitter

"Kun san cewar an fitar da suna na cikin jerin sunayen 'yan takarar da aka tantance amma daga baya aka sake fitar da wani jerin sunayen babu na wa a ciki," a cewar Abba.

Sannan ya cigaba da cewa, "yanzu ba lokacin surutai da yawa bane; wannan lokaci ne na addu'a, kuma ina son ku taya ni rokon Allah ya cire duk wani mai ja da ikon ubangiji daga hedkwatar jam'iyyar APC. Allah ka san ko su waye, ka yi mana maganinsu."

DUBA WANNAN: 'Yan takarar PDP 5 da har yanzu basu taya Atiku murnar samun nasara ba

"Ya Allah duk wani shugaba dake rike da mukami a APC kuma ba ya aiki da akidu da manufofinta, Allah kar ka ba shi ikon lalata jam'iyyar," a addu'ar Abba.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya cire Abba daga mukaminsa na shugaban rundunar 'yan sanda bayan kammala zaben shekarar 2015 bisa zarginsa da nuna goyon baya ga shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel