Sarki Sanusi ya soki salon mulkin Shugaba Buhari a kaikaice

Sarki Sanusi ya soki salon mulkin Shugaba Buhari a kaikaice

A wani salo irin na azanci, tsohon shugaban babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya caccaki salon mulkin da ake gudanarwa a Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari.

Sarkin na Kano ya bayyana cewa idan dai har ba'a dauki muhimman matakai ba a cikin lokaci, to lallai kasar ta Najeriya zata dade tana jagorantar kasashen duniya a fannin talauci da kuncin rayuwa.

Sarki Sanusi ya soki salon mulkin Shugaba Buhari a kaikaice

Sarki Sanusi ya soki salon mulkin Shugaba Buhari a kaikaice
Source: UGC

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga gare mu - Kwankwaso

Legit.ng ta tsinkayi Sarkin yana wannan jawabin a cikin wata makala da ya gabatar a jami'ar tarayya ta garin Ibadan inda ya bayyana cewa idan dai har aka cigaba da tafiya a haka, to a shekarar 2050, lamarin ba zai yi dadi ji ba.

Sarki Sanusi ya kara da cewa idan dai har ba'a gyara ba, to nan da shekarar 2050 sama da kashi 80 na matalautan duniya za su kasance ne a nahiyar Afrika kuma a cikin su fiye da rabi za su kasance ne a Najeriya da kuma kasar Congo.

A wani labarain kuma, Kwamitin dake ke alhakin gudanar da zabe da uwar jam`iyyar APC daga Abuja ta tura jihar Zamfara ya sanar da cewa jihar ta tashi ba ta da ko da dan takara daya sakamakon rashin samun damat gudanar da zaben fiitar da gwanin da yayi har lokacin cikar wa'adin da hukumar zabe ta sa na mika sunayen 'yan takara.

Wannan dai kamar yadda muka samu ya faru ne sakamakon shafe fiye da sati daya ana kokarin gudanar da zaben amma hakan bai samu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel