‘Yan takarar PDP 5 da har yanzu basu taya Atiku murnar nasarar da ya samu ba

‘Yan takarar PDP 5 da har yanzu basu taya Atiku murnar nasarar da ya samu ba

A yayin da ake cigaba da mahawara da cece-kuce a kan nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya samu a zaben cikin gida na jam’iyyar PDP, jama’a sun lura cewar har yanzu akwai wasu daga cikin ‘yan takarar da Atikun ya kayar da basu taya shi murnar nasarar day a samu ba.

A jiya ne aka bayar da sanarwar cewar Atiku, mai shekaru 72, ya samu kuri’u 1,532 da suka ba shi dammar kayar da ragowar ‘yan takara 11 da suka tsaya neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Ragowar ‘yan takarar da Atiku ya kayar sun hada da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da takwaransa na jihar Jigawa, Sule Lamido, da tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang, gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da tsohon shugaban majalisar dattijai, David Mark.

‘Yan takarar PDP 5 da har yanzu basu taya Atiku murnar nasarar da ya samu ba

Atiku Abubakar
Source: Depositphotos

Ragowar su ne Datti Baba Ahmed, Stanley Osifo, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya zo na biyu a zaben.

Ya zuwa yanzu, wasu daga cikin ‘yan takarar sun taya Atiku murnar samun nasara da ya yi a zaben.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya za ta sanar da sabon karin albashi - Shugaban kungiyar kwadago

Daga cikin manyan ‘yan takarar da ba a ji daga bakinsu ba har ya zuwa yanzu akwai; tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel