Sanata Dino Melaye da Smart Adeyemi za su gwabza a zaben 2019

Sanata Dino Melaye da Smart Adeyemi za su gwabza a zaben 2019

Mun fahimci cewa Sanata Dino Melaye na iya rasa kujerar sa a Majalisar Dattawa kamar yadda mu ka samu labari. Fitaccen Sanatan dai zai gwabza ne a zaben 2019 da wani tsohon Sanata watau Smart Adeyami.

Sanata Dino Melaye da Smart Adeyemi za su gwabza a zaben 2019

Sanata Smart Adeyemi na neman dawowa kujerar sa a Majalisa
Source: Depositphotos

Sanata Dino Melaye ne yayi nasara a zaben fitar da gwani na Jam’iyyar adawar PDP da kyar sai dai kuma zai kara da ‘Dan takarar da ya doke a 2015 watau Sanata Adeyemi. A wancan lokaci dai Adeyami yana PDP ne yayin da Dino yake APC.

Manyan ‘Yan Majalisar dai za su fafata ne a zaben 2019 bayan karawar da su kayi a 2015. A yanzu dai ‘Yan Majalisun sun sauya-sheka inda Adeyemi ya koma Jam’iyyar APC yayin da Dino Melaye da wasu Sanatoci su ka koma Jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Mark zai bar Majalisa bayan shekaru kusan 20

A 2015 ne dai Smart Adeyami ya sha kasa wajen Melaye wanda ya rikewa Jam’iyyar APC tuta a zaben Majalisar Dattawa na Mazabar Kogi ta Yamma. Yanzu dai Adeyami ya samu tutar APC bayan ya doke Toyin Akanle da kuri’a 1893.

A Yankin Kogi ta Gabas dai Jibrin Isah ne yayi nasara inda Yakubu Oseni ya samu tikitin APC a Kogi ta Tsakiya. Clement Olafemi, Henry Ojuola, da Oreniya Salaudeen su na cikin wadanda Dino Melaye ya buge wajen samun kujerar Sanata.

Fitaccen ‘Dan Majalisar Najeriya Dino Melaye na iya rasa kujerar sa. An kama hanyar canza gari tsakanin Dino Melaye da Adeyemi. Yanzu dai sai Dino Melaye yayi da gaske zai koma kujerar sa a Majalisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel