Magoya bayan Mama Taraba 50,000 sun fice daga APC sun koma UDP

Magoya bayan Mama Taraba 50,000 sun fice daga APC sun koma UDP

- Magoya bayan tsohuwar Ministan Harkokin Mata, Aisha Alhassan 5,000 sun fice daga APC zuwa UDP a jihar Taraba

- Sun bayyana cewa sun baro APC ne saboda rashin adalci da jam'iyyar ke musu

- A jawabinta na karbarsu, Aisha Alhassan ta tabbatar musu da cewa za ayi musu adalci a UDP

Tsohuwar Ministan Harkokin Mata kuma 'yar takarar gwamna karkashin jam'iyyar United Democratic Party (UDP) a jihar Taraba, Sanata Aisha Alhassan wanda akafi sani da Mama Taraba ta karbi magoya bayanta 50,000 da suka baro APC zuwa UDP a ranar Litinin.

Magoya bayan Mama Taraba 50,000 sun fice daga APC sun koma UDP

Magoya bayan Mama Taraba 50,000 sun fice daga APC sun koma UDP
Source: Twitter

A taron karbar sabbin mambobin da aka gudanar a dakin taro na Unity da ke Jalingo, Alhassan ta tabbatarwa magoya bayanta cewar za ayi musu adalci a jam'iyyar UDP.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP

Jagoran wadanda suka sauya shekar kuma tsohon jigo a jam'iyyar APC a jihar, Uba Mairiga ya ce rashin adalci da aka yi masa da magoya bayansa ne ya sa suka fice daga jam'iyyar APC.

Mairiga ya shiga takarar dan majalisar jiha na yankin Jalingo II a APC amma aka kayar da shi a zaben fidda gwani, yanzu kuma ya sake sayan fom din takara na mazabar karkashin jam'iyyar UDP.

"Ni da magoya baya na mun baro APC kuma za mu bayar da gudunmawarmu domin ganin UDP ta yi nasara a dukkan zabukkan da za'ayi a jihar," inji shi.

A bangarensa, gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya taya Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar muranar lashe zaben fidda gwani da shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel