Yanzu Yanzu: Fayose yayi barazanar barin PDP

Yanzu Yanzu: Fayose yayi barazanar barin PDP

Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti yayi barazanar sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan na zuwa ne bayan babban taron jam’iyyar wada aka gudanar a ranar Asabar, 6 ga watan Oktoba a jihar Rivers.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya fadi haka ne a ranar Litinin, 8 ga watan Oktoba.

Yanzu Yanzu: Fayose yayi barazanar barin PDP

Yanzu Yanzu: Fayose yayi barazanar barin PDP
Source: Depositphotos

An tattaro cewa gwamnan yace da zaran ya kammala tuntuba zai yi Magana ga ‘yan Najeriya a warware.

KU KARANTA KUMA: 2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa

A baya Legit.ng daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Jonah Jang, ya taya Atiku Abubakar murna a kan nasarar da ya samu a kan su.

Sannnan kuma ya yi alkawin goya masa baya har ya samu nasara. Jang ya yi wannan sanarwar taya murna da alkawarin goyon baya ne a cikin wata takarda da ya raba wa manema labarai, a Jos, Babban birnin jihar Plateau.

Jang, wanda ya zo na biyun na karshe da kuri’u 19, ya bayyana Atiku a matsayin shugaban da ke jira kawai a rantsar da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel