Shehu Sani ne kadai dan takarar da muka sani a Kaduna ta Tsakiya - APC

Shehu Sani ne kadai dan takarar da muka sani a Kaduna ta Tsakiya - APC

Uwar jam'iyyar ta All Progressives Congress(APC) ta ce Sanata Shehu Sani ne kadai dan takarar da jam'iyyar ta sani daga mazabar Kaduna ta Tsakiya.

Sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar, Mr Yekini Nabena ne ya bayar da wannan sanarwan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja ranar Lahadi.

Ya ce Sani ne kadai dan takarar da uwar jam'iyyar ta san da zaman sa daga yankin Kaduna ta tsakiya.

Shehu Sani ne kadai dan takarar da muka sani a Kaduna ta Tsakiya - APC

Shehu Sani ne kadai dan takarar da muka sani a Kaduna ta Tsakiya - APC
Source: Twitter

Sanata Shehu Sani ya nisanta kansa daga zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Kaduna ranar Asabar inda aka ruwaito cewar mai bawa gwamna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin siyasa, Malam Uba Sani ne ya lashe zaben.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

Jami'in zabe na zaben fidda gwanin da akayi a Murtala Muhammed Square Kaduna, Farfesa Eddie Floyd-Igbo, ya sanar cewar Uba Sani ne ya lashe zaben da kuri'u 2,088 yayin da Shehu Sani ya samu kuri'u 15 kacal.

Wani dan takarar kujerar, Usman Ibrahim Sardauna ya samu kuri'u 129.

Sai dai duk da hakan, Nabena ya sake jadadawa cewar Shehu Sani ne kadai dan takarar da uwar jam'iyya ta tantance a matayin dan takarar Sanata daga mazabar Kaduna ta Tsakiya zone 2.

Ya ce anyi zaben a yankin Kaduna ta Tsakiya amma Majalisar Wakilai na tarayya da majaliar wakilai na jihar amma maganan zaben kujerar Sanata, Shehu Sani ne kadai dan takarar jam'iyyar.

Ya ce gwamnan jihar ba shine zai rika juya jam'iyyar yadda ya so ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel